Mr Ban wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ta hannun kakakinsa ya bayyana cewa, wannan muhimmin mataki ne na kawo karshen tashin hankalin da ya cusa al'ummar kasar cikin akuba.
Babban sakataren MDDr ya kuma yaba wa kungiyar IGAD bisa kokarin ta na ganin kammalar tattaunawar cikin nasara. Mr Ban ya bayyana farin cikinsa kan hadin kan da shugabannin shiyyar suka nuna na ganin an kawo karshen wannan tashin hankali.
A makon da ya gabata ne shugaban 'yan tawaye Riek Machar ya sanya hannu kan yarjejeniyar yayin da shugaba Kiir ya ki sanya hannu a yarjejeniyar.
Sanya hannun da shugaba Machar din ya yi alama ce da ke nuna kawo karshen fadan da dakarun bangarori biyu ke yi, yayin da Riek Machar zai koma kan mukaminsa na mataimakin shugaban kasar Sudan ta kudun wadda ta samu 'yancinta a shekara 2011 daga kasar Sudan.(Ibrahim)