in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 7 sun rasu sanadiyyar harin da aka kai ga wata mashaya dake tsakiyar Mali
2015-08-08 14:01:18 cri
Jiya Jumma'a 7 ga wata, wasu dakarun da ba a tantance ko su waye ba sun kai hari a wata mashaya dake birnin Sevare dake tsakiyar kasar Mali, wanda ya haddasa rasuwar mutane a kalla guda 7, kuma a lokacin, wasu ma'aikatan MDD na cikin wannan mashaya.

Bisa labarin da gwamnatin kasar Mali ta bayar, an ce, a lokacin da dakarun suka kai hari a mashayar, wasu ma'aikatan tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a kasar Mali suna zama a wannan mashaya. Bayan aukuwar harin, nan da nan, rundunar sojan kasar Mali ta aike da sojojin musammun zuwa wurin, inda suka yi musayar wuta da dakarun da suka kai harin, da yi ma mashayar kawenya.

Harin dai ya haddasa a kalla mutuwar sojojin kasar Mali guda biyar, tare da jikkata biyu, haka kuma maharan biyu an bindige su har lahira.

Cikin sanarwar da gwamnatin kasar Mali ta fidda, ba ta ambace asalin dakarun da suka kai wannan harin ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China