Sanarwar ta bayyana cewa, Ban Ki-moon ya nuna damuwa sosai kan hali mai tsanani da ake ciki a wasu yankuna dake arewacin kasar Mali, ciki har da rikice-rikicen da dakaru suka tada.
Ban Ki-moon ya nuna cewa, wadannan rikice-rikice sun saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a Ouagadougo a watan Yuni na shekarar 2013 da kuma irinta da aka daddale a ranar 23 ga watan Mayu na bana.
Don haka ya yi kira ga bangarori daban daban da abin ya shafa da su dakatar da yake-yake da juna, kana su yi hadin gwiwa da hadadden kwamitin tsaro da ke karkashin jagorancin tawagar kiyaye zaman lafiya ta MDD da ke Mali. A cewar Ban ki-Moon, wannan matakin zai taka muhimmiyar rawa ga tattaunawar neman samun sulhuntawa da ake yi a tsakanin bangarori daban daban na kasar Mali,
A ranar 16 ga wata ne, gwamnatin kasar Mali da dakaru masu adawa suka fara yin shawarwari a tsakaninsu a birnin Algeis, babban birnin kasar Algeria, inda suka sanya hannun kan yarjejeniyar sulhu a tsakanin sassa daban-daban na kasar a ranar 24 ga wata. Hakan ana sa ran ganin kawo karshen tashe-tashen hankali da ake fama da su a arewacin kasar. Saidai bangarorin biyu za su kaddamar da wani sabon shawarwari a tsakiyar watan Agusta na bana. (Zainab)