Bangaren sojin Mali da ke a yankin ya fayyace cewa, an kai hari ne da sanyin safiyar jiya Litinin, amma har yanzu ba a tabbatar da waye ya kai harin ba.
A cikin 'yan shekarun nan dai ana ci gaba da dauki ba dadi a yankin arewacin kasar ta Mali. A kuma ranar 15 ga watan Mayu sojojin gwamnatin Mali da dakarun dake dauke da makamai da ke yankin arewacin kasar suka daddale yarjejeniyar samar da zaman lafiya, a birnin Bamako, sai dai muhimman rukunonin 'yan adawa 3 na dakarun MNLA na kasar ba su halarci bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ba.
A kuma ranar 20 ga watan Yuni, wakilan kungiyar MNLA sun kai ga sa hannu a yarjejeniya, matakin da ya nuna cewa an daddale yarjejeniyar zaman lafiya a kasar ta Mali, ko da yake hakan bai sanya an dakatar da kaiwa sojojin Malin hare-hare a kai a kai ba. (Bako)