Nesirky yayi bayanin cewa an sanar ofishin kiyaye zaman lafiya na majalisar cewa Nijeriya zata janye wasu dakarunta na soji,yana mai bayanin cewa sai dai hakan ba ya nufin gaba daya ba,domin za ta bar wasu da suka hada da sojoji ma'aikatan kiwon lafiya da 'yan sanda.
Kakakin a don haka ya isar da sakon godiya ga kasar Nijeriya bisa ga taimakon da ta rika bayarwa kawo yanzu ga ayyukan kiyaye zaman lafiya na majalisar.
Ya kara da cewa ofishin kula da ayyukan kiyaye zaman lafiya na cigaba da tuntubar sauran kasashe don su bada gudumuwar rundunar su ga ayyukanta a kasar Mali.
A watan Fabrairu ne Nijeriya ta aika da sojoji 1,200 zuwa ga rundunar kasashen Afrika ta tallafawa Mali AFISMA a matsayin gudummuwarta ga ayyukan kiyaye zaman lafiya a kasar Mali. A watan Afrilu kuma kwamitin tsaro na MDD ta amince da rundunar kiyaye zaman lafiya na majalisar MINUSMA mai sojoji fiye da 12,600 da ta karbi ragamar jagoranci daga hannun AFISMA,abin da yasa a ranar 1 ga watan Yuli aka kammala ayyukan musayar jagoranci tsakanin rundunar guda biyu a Bamako babban birnin kasar Mali.Yanzu haka MINUSMA ce rundunar mafi girma ta uku na majalisar a duniya.(Fatimah Jibril)