Cikin jawabin ta Madam Liu, ta ce shekaru 6 bayan kaddamar da tsarin shawarwari na musayar al'adu tsakanin kasashen Sin da Amurka, saurin bunkasuwar mu'amalar bangarorin biyu ya haura yadda aka zato, kuma musayar al'adu, da amincewar juna a fannin siyasa, da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, sun zama manyan ginshikai uku na raya huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka.
A yayin shawarwari na wannan zagaye, bisa kuma taken sa na "mu'amala da yin koyi da juna, da hadin gwiwar moriyar juna", kasashen Sin da Amurka sun daddale yarjejeniyoyi 119 dake kunshe da fannonin ilmi, da kimiyya da fasaha, da al'adu, da kiwon lafiya, da wasanni, da harkokin mata da matasa.
Madam Liu ta ce, idan aka yi duba na tsanaki, ya kamata a yi amfani da musayar al'adu, don karfafa, da yaukaka, da yalwata dangantakar bangarori biyu, don raya sabon nau'in dangantakar Sin da Amurka.
Daga bangaren Amurka kuwa, wakilan kasar sun bayyana cewa akwai makoma mai haske game da raya dangantakar dake tsakanin kasashen Amurka da Sin, kuma ya kamata bangarorin biyu su kara fadada musayar al'adu a tsakaninsu, don sa kaimi ga fahimtar juna da amincewa da juna, da raya dangantakar abokantaka, karkashin tsarin girmama juna, da samun amincewar juna, matakin da zai yi amfani matuka ga samar da zaman lafiya da wadata a duniya. (Bako)