in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan jami'an Sin da Amurka sun tattauna kan manyan tsare-tsare a Washington
2015-06-25 19:38:34 cri

Daga ranar 23 zuwa 24 ga wata ne, kasashen Sin da Amurka suka gudanar da taron tattaunawa dangane da manyan tsare-tsare da tattalin arziki karo na 7 a birnin Washington, hedkwatar kasar Amurka.

Yang Jiechi, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, da John Kerry, sakataren harkokin wajen Amurka kuma manzon musamman na shugaba Barack Obama na Amurka ne suka shugabanci taron, inda bangarorin 2 suka tattauna kan raya sabuwar huldar da ke tsakanin kasashen 2, zurfafa hadin gwiwar a-zo-a-gani a tsakaninsu, inganta hada kansu a yankin Asiya da tekun Pasific, daidaita batutuwan shiyya-shiyya da kalubalolin da kasashen duniya ke fuskanta, shawo kan sabanin da ke tsakaninsu yadda ya kamata da dai sauransu, kana a karshe suka cimma yarjejeniyoyi fiye da 120.

A yayin taron, manyan jami'an kasashen 2 sun waiwayi kyakkyawan ci gaban da aka samu wajen bunkasa huldar da ke tsakanin Sin da Amurka a shekarun baya, sun kuma yarda da ci gaba da aiwatar da ra'ayoyin da shugabannin kasashen 2 suka cimma a baya, a kokarin sa kaimi kan kyautata sabuwar dangantakar da ke tsakaninsu. Har wa yau bangarorin 2 na ganin cewa, ziyarar aiki da shugaba Xi Jinping zai kai wa Amurka a watan Satumban bana bisa gayyatar da takwaransa mista Obama ya yi masa, tana da muhimmiyar ma'ana, don haka tabbatar da kammala ziyararsa cikin cikakkiyar nasara zai dace da moriyar kasashen 2 duka. Don haka kamata ya yi bangarorin 2 su taimakawa juna sosai wajen share fagen wannan ziyara. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China