Bugu da kari, ya ce, a ganin Sin, babu shakka akwai bambancin ra'ayoyi har ma da 'yan sabani tsakanin kasashen biyu, amma ba su hana bunkasuwar dangantakar kasashen biyu ba, musamman ma a halin yanzu, ana ci gaba da habaka hadin gwiwar dake tsakaninsu, haka kuma, kasashen biyu suna iya cimma ra'ayi daya kan wasu batutuwa ta hanyar yin shawarwari, sa'an nan suna kuma kokarin inganta hadin gwiwar dake tsakaninsu domin cimma moriyar juna da kuma fuskantar kalubalolin da duniya ke fuskanta cikin hadin gwiwa. (Maryam)