Daga ranar 23 zuwa 24 ga wata ne, manyan jami'an kasashen Sin da Amurka suka yi taron tattaunawa ta fuskar al'adu karo na 6 a birnin Washington, hedkwatar kasar Amurka, inda madam Liu Yandong, mataimakiyar firaministan kasar Sin kuma manzon musamman ta shugaba kasar Sin Xi Jinping ta halarta tare da yin jawabi, kana shi ma Tony Blinken, mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka ya halarci taron.
A yayin taron, bangarorin 2 sun waiwaiyi yadda tsarin gudanar da taron tattaunawa tsakanin manyan jami'an Sin da Amurka ta fuskar al'adu karo na 6 yake kara inganta yin mu'amala a tsakanin kasashen 2 ta fuskar al'adu tun bayan kafuwarsa shekaru 5 da suka gabata. Har wa yau sun amince da kokarin da gwamnatoci da hukumomin kasashen 2 suke yi, tare da yin kira da a kara kokarin zurfafa hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen 2.
Haka zalika bangarorin 2 sun tattauna batutuwan da suka shafi ba da ilmi, kimiyya da fasaha, al'adu, kiwon lafiya, wasannin motsa jiki, mata, matasa da dai sauransu, ko da ya ke batun kiwon lafiya sabon abu ne a wannan karo. Manyan jami'an sun kuma nazarci yadda kasashen 2 suka hada kansu a shekara guda da ta gabata, tare da tattaunawa kan manufar da za su bi a nan gaba.
Baki daya bangarorin 2 sun cimma daidaito kan batutuwa 199 a fannoni 7 a yayin taron. (Tasallah Yuan)