Ren Minghui ya bayyana hakan ne a birnin Washington na kasar Amurka a jiya Laraba, yayin gun taron manema labaru a wani bangare na shawarwari da ake gudanarwa game da al'adu a tsakanin Sin da Amurka zagaye na shida. Ya ce kungiyar hadin kan Afirka ta AU ta amince da kara sa ido ga barkewar cututtuka a yankin, musamman a gabar da ake fuskantar yaduwar cutar Ebola.
Tun daga karshen shekarar bara kuma, kungiyar AU da gwamnatin kasar Sin, tare da gwamnatin kasar Amurka, da kuma cibiyoyin yaki da cututtuka na kasashen biyu, sun yi shawarwari kan yadda za a tsara wani shirin rigakafi da yaki da cututtuka a nahiyar Afirka.
Ren ya kara da cewa kungiyar AU, ta tura tawagar musamman domin bincikar cibiyar rigakafi da yaki da cututtuka ta kasar Sin, da tsarin sa ido ga faruwar cututttuka na kasar ta Sin. Haka zalika kuma, AU ta daddale takardar fahimtar juna kan kafa cibiyar rigakafi, da yaki da cututtuka a nahiyar Afirka, tare da cibiyar rigakafi da yaki da cututtuka ta kasar Amurka.
Yanzu haka bangarorin uku suna tattaunawa game da yadda za a dada goyon baya ga tsarin gina irin wannan cibiya a nahiyar Afirka bisa shiri na bai daya. (Zainab)