in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi: Kamata ya yi a maida kiyaye teku a matsayin abun da zai inganta hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka
2015-06-25 11:26:15 cri
A jiya Laraba ranar 24 ga wata ne aka shirya wani taron musamman game da kiyaye harkokin teku takanin kasashen Sin da Amurka, a karkashin tsarin tattaunawa kan manyan tsare-tsare, da tattalin arziki karo na 7 tsakanain kasashen biyu, taron da ya samu halartar manzon musamman na shugaban kasar Sin, kuma wakilin majalisar gudanarwar kasar Yang Jiechi, da manzon musamman na shugaban kasar Amurka kuma sakataren harkokin wajen kasar John Kerry.

A yayin taron wanda ya gudana a birnin Washington, Yang Jiechi ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen Sin da Amurka su karfafa kokarinsu, da nufin mayar da batun kiyaye harkokin teku a matsayin sabon lamari da zai inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Baya ga hakan, Yang ya jaddada cewa, kamata ya yi kasashen biyu su kara fadada cudanya da gudanar da shawarwari, da tattaunawa game da hadin kan su a fannonin kiyaye muhallin halittun teku, da bincike kan muhallin teku, da kiwo, da kiyaye albarkatun aikin su da dai sauransu. Har wa yau ya dace a kara bunkasa mu'amala tsakanin hukumomin dake lura da amfani da teku na kasashen biyu, domin daga matsayin hadin gwiwa ta fuskar murkushe ayyuka ba bisa doka ba, da gudanar da ayyukan ceto na jin kai, da kuma gudanar da harkokin sufurin abubuwa masu hadari a teku.

Bugu da kari za a fadada cudanya tsakanin kasashen biyu, kan batutuwan da suka shafi dokokin teku, da harkokin yanki mafi sanyi na "polar region" da makamantansu, ta yadda za a inganta wadata da dauwamammen ci gaba a teku.

A nasa bangaren, Kerry ya bayyana cewa, kasar Amurka na fatan kokari tare da Sin wajen gudanar da hadin kai a fannonin amfani da dokoki, da neman ci gaba mai dorewa da dai sauransu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China