in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in Sin ya nuna rashin jin dadi game da sabuwar dokar tsaron Japan
2015-07-16 21:16:17 cri

Mamba a majalissar gudanarwar kasar Sin Mr Yang Jiechi, ya zanta da darektan hukumar tabbatar da tsaron kasar Japan Syotaro Yachi, wanda ke ziyarar aiki a nan kasar Sin a yammacin ranar Alhamis din nan.

A yayin zantawar ta su wadda ta kunshi batutuwa da dama, ciki hadda na harkokin siyasa, Mr. Yang ya bayyana rashin jin dadi game da zartas da dokar tsaron Japan da aka yi, wadda ta tanaji baiwa sojin Japan din damar fafatawa a wajen kasar.

Rahotanni sun nuna cewa majalisar wakilan kasar ta Japan ta kira wani babban taro, inda mambobin ta daga jam'iyyu biyu dake mulki, suka tilasa zartas da wannan doka, ta amfani da rinjayen su a majalisar.

Jam'iyyun adawa da dama sun nuna rashin jin dadi kan wannan dayen aiki. Kana yawancin jama'ar kasar suma basu amince da hakan ba.

Mr. Yang Jiechi ya ce kullum matakan da sojan Japan ke dauka na matukar janyo hankalin makwabtan kasar, da ma sauran kasashen duniya, saboda dalilai na tarihi.

Wannan ne dai karo na farko da aka zartas da irin wannan doka wadda ta shafi aikin soji a majalisar wakilan kasar, tun bayan yakin duniya na biyu.

Kaza lika Mr. Yang ya nanata cewa, wannan shekara da muke ciki, ita ce ta cika shekaru 70 da samun nasarar yakin kin 'yan facist a duniya, don haka Sin ke kalubalantar Japan da ta koyi darasi daga tarihi, ta kuma rungumi hanyar samun ci gaba cikin lumana, tare kuma da mutunta abubuwan da makwabtanta ke mai da hankali a kan su, kana kada a dauki mataki da zai kawo illa ga zaman lafiya da lumana a wannan yanki.

A daya hannun, a dai wannan rana kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana matsayin Sin game da wannan doka da Japan ta zartas. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China