Mr. Yang ya bayyana hakan ne ya yin da yake zantawa da ministan tsaron kasar Afirka ta Kudu David Mahlobo a jiya Litinin 25 ga wata a birnin Moscow. Ya ce Sin na dora muhimmancin gaske ga alakar da ke tsakanin ta da Afrika ta Kudu. Kana ta na fatan ci gaba da fadada hadin gwiwa tsakanin sassan biyu a mataki na M.D.D, da kungiyar kasashen da ke samun saurin bunkasuwa ta BRICS, da kungiyar manyan kasashe masu tasowa da ke da burin bunkasuwa a matakin farko, domin kiyaye hakkokin su tare.
Mr. Yang ya kara da cewa Sin tana fatan hadin gwiwa tare da abokan ta na Afrika, wajen raya zamantakewar al'umma, da tattalin arziki a nahiyar Afrika, a wani mataki na goyon baya game da aikin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar.
A nasa bangare, Mr. Mahlobo ya ce kamata ya yi a inganta hadin gwiwa dake tsakanin sassan biyu wajen raya muhimman ababen more rayuwa, da samar da zaman lafiya da tsaro, da horar da ma'aikata, da tsaron tashar Internet, da yaki da aikata laifuffuka a kasashe daban daban. (Bako)