Mamba a hukumar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi, ya ce kasar sa na fatan inganta hadin gwiwa da Uganda, domin ganin an aiwatar da manyan yarjeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da fadada mu'ammala tsakaninsu, da karfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, da ingiza hadin gwiwa, da sa kaimi ga hadin kan masana'antu daban-daban na kasahen biyu. Sauran sassan sun hada da habaka mu'ammala ta fuskar al'adu, da karfafa hadin gwiwar tsakanin kasa da kasa, da kuma zurfafa hadin kan kasashen biyu a dukkanin fannoni.
Mr. Yang ya bayyana hakan ne a jiya Talata, ya yin ganawar sa da Shugaba Yoweri Museveni na kasar Uganda.
Da yake maida jawabi shugaba Museveni, ya bayyana matukar godiya game da taimakon da Sin take baiwa Uganda cikin dogon lokaci. Ya ce kasar sa tana fatan kara yin hadin gwiwa a fannoni daban-daban da kasar Sin, ta yadda al'ummun bangarorin biyu za ci gaba da samun bunkasuwar tattalin arziki tare karkashin dangantakar dake tsakaninsu.
Ya yin ziyarar sa a Uganda Mr. Yang ya kuma gana da firaministan kasar Ruhaka Rugunda, a birnin Kampala helkwatar kasar ta Uganda. (Amina)