Yang Jiechi ya bayyana cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin murnar cika shekaru 70 da cimma nasarar kare kasar Rasha, ya kuma kai ziyarar aiki kasar ta Rasha, bisa gayyatar shugaba Vladimir Putin, inda shugabannin biyu suka tabbatar da makomar bunkasuwar dangantakar kasashen su, da hadin gwiwarsu, tare da tsaida kudurin kara goyawa juna baya, game da manyan batutuwan dake shafar moriyarsu, da karin hadin gwiwar su a harkokin kasa da kasa da na yankuna.
A nasa bangare, Patrushev ya bayyana cewa, yanzu haka an shiga yanayi mafi kyau game da raya dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha. Kaza lika kasashen biyu na hadin gwiwa karkashin inuwar kungiyar BRICS, da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, da kuma manyan batutuwan kasa da kasa da na yankuna. Har wa yau sun ki amincewa da yunkurin da wasu bangarori ke yi na kawo illa ga nasarorin da aka samu bayan yakin duniya na biyu. (Zainab)