Mr. Yang Jiechi ya bayyana hakan ne a jiya Juma'a, cikin jawabin da ya gabatar, ya yin bude taron tsaro na Munich karo na 51.
Mr. Yang ya bayyana cewa, bana ta cika shekaru 70 da kawo karshen yakin duniya na biyu, da kuma kafa MDD. Ya ce cikin wadannan shekaru 70, yanayin zaman lafiya ya tabbata a duniya. Duk da haka, ya kamata a lura da matsalolin da ake fuskanta wajen farfado da tattalin arzikin duniya, da rashin kwanciyar hankali a wasu sassan duniya da kuma karuwar barazanar ayyukan ta'addanci.
A sabili da haka, Mr. Yang ke ganin cewa ya zama dole, a ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya, da sa kaimi ga samun bunkasuwa tare cikin dogon lokaci.
Yang ya kara da cewa, Sin na cikin jerin kasashen duniya dake kokarin sauke nauyin dake kan su, kuma za ta kara kwazo a fannin tabbatar da zaman lafiya, da sa kaimi ga samun bunkasuwa tare.
Ya ce, makomar sauran sassan duniya ma ya shafi makomar kasar Sin. Don haka take fatan ci gaba da hadin gwiwa tare da sauran kasashe, a kokarin samar da makoma mai kyau a fannin wanzar da zaman lafiya da samun ci gaba tare.
Taron na bana dai ya samu halartar wakilai sama da 400, daga kasashe sama da 50, ciki hadda ministan tsaron kasar Jamus Ursula von der Leyen, da babban sakataren kungiyar NATO, Jens Stoltenberg wadanda suka gabatar da jawabai ya yin bikin bude taron.(Fatima)