Mamban majalissar gudanarwar kasar Sin Mr Yang Jiechi, ya yi jawabi don gane da batun ziyarar da firaminsitan kasar Japan Shinzo Abe ya kai Haikalin Yasukuni a ranar Asabar 28 ga watan nan.
Mr Yang ya ce hakan ya nuna halin ko in kula da Firaministan kasar Japan ya nuna, game da ra'ayin al'ummun sauran kasashe, musamman wadanda suka sha fama da tasirin nuna karfin soja, da mulkin mallakar da Japan ta yi musu a baya.
Har wa yau a cewar Mr Yang hakan tamkar tsokana ce ga al'ummun duniya, masu ra'ayin zaman lafiya. Bugu da kari ziyarar ta Abe ta nuna alamun rashin martaba adalci, da mutuncin Bil Adama, kuma mataki ne na takala da Japan ta yi, wanda ka iya gurgunta yanayin doka da oda tsakanin kasa da kasa. Yace ba daidai ba ne a aikata duk wani abu da zai lalata yanayin da ake ciki bayan tarihin da ya riga ya wuce yayin yakin duniya na biyu, bisa ci gaba da aka samu na yaki da tunanin son tada husuma da mulkin mallaka da Japan ke da shi a da. Don gane da haka ko shakka babu, gwamnatin kasar Sin da kasashen duniya za su ci gaba da yin Allah wadai ga wannan mataki da Shinzo Abe ya dauka.
Mr Yang ya kuma jaddada cewa ba wani mutumi da zai iya muzanta Sinawa. Ya ce kamata ya yi Shinzo Abe ya amince da kuskure da ya yi, ya kuma dauki matakan gyara. Yace Sin na shawartar sa da kaucewa almundahana, muddin yana fatan samun amincewar kasashen makwabta, da duniya baki daya. (Amina)