Mamba a majalisar zartaswar kasar Sin Yang Jiechi ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da shugaban zaman Majalisar, kuma tsohon ministan ma'aikatar harkokin wajen kasar Sabiya Vuk Jeremic a jiya Jumma'a. Mr. Yang ya kara da bayyana bukatar dorewar rawar da MDD ke takawa, a fagen inganta dangantakar kasa da kasa.
Da yake tsokaci don gane da alakar Sin da kasar Sabiya kuwa, Mr. Yang ya ce bangarorin biyu na samun ci gaba a wannan fage cikin 'yan shekarun nan, ya kuma bayyana fatan aiwatar da daukacin yarjeniyoyin da shuwagabannin kasashen biyu suka cimma, domin bunkasar dangantakar dake tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi.
A nasa jawabi Vuk Jeremic, cewa ya yi Sabiya da Sin abokai ne na hakika, don haka akwai bukatar dorewar hadin kansu a dukkanin fannonin ci gaba. (Saminu Alhassan)