in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 12 sun rasu sakamakon fashewar bututun man fetur a Nijeriya
2015-07-11 13:31:33 cri
Jiya Jumma'a 10 ga wata, kamfanin man fetur na Eni na kasar Italiya ya tabbatar da cewa, wani bututun man fetur na kamfanin dake kudancin kasar Nijeriya ya fashe a yayin da aka yi masa gyara a ran 9 ga wata, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane 12, yayin da 3 suka jikkata.

Kuma wani wakilin kamfani ya bayyana cewa, fashewar din ta faru ne a jihar Bayelsa, mutanen 12 da suka rasu dukkansu ma'aikatan da ke gyara bututun ne, kana ana gudanar da bincike kan dalilin da ya haddasa hadarin a halin yanzu.

Kana wani jami'in kasar ya ce, an riga an kai wadanda suka ji rauni zuwa asibiti, biyu daga cikinsu suna fama da kunar jiki mai tsanani.

Kasar Nijeriya na da albarkatun man fetur, kamfanin Eni na kasar Italiya ya kafa wani kamfani tare da abokan zuba jari a kasar, domin hakar man fetur cikin hadin gwiwa a cikin wannan kasar dake yammacin Afrika. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China