Rahotanni sun ce ministan harkokin wajen Birtaniya Philip Hammond, ya shaidawa Buhari firaministan kasar Birtaniya David Cameroon game da halartar sa taron na G7, yayin bikin rantsuwar kama aikin da aka gudanar a Abuja, a ranar 29 ga watan Mayun da ya shude.
Firaministan kuma na sa ran shagaba Buhari zai halarci taron inda zai gabatar da wasu kudurori game da Najeriya.
Kafin hakan, a 'yan kwanakin baya yayin ganawar sa da firaministan Birtaniya a birnin London, Mr. Cameroon ya alkawarta baiwa Nijeriya taimako, musamman a fannin yaki da masu tsattsauran ra'ayi, da dakile bakin haure na haram daga kasashen Afrika. A sa'i daya kuma, David Cameroon yana sa ran Buhari zai sa hannu kan yarjejeniyar raya dangantakar abokantaka, ta tattalin arziki da ke tsakanin kungiyar EU da Afrika, wadda tuni kasashen Afrika da dama suka amince da ita.(Bako)