Faduwar farashin man fetur, matsala ce ga Rasha, Venezuela, Nijeriya da sauran wasu kasashe, wadanda suke fuskantar babbar matsin lamba a fannin kudi a sakamakon raguwar farashin man fetur.
Game da wannan labarin da aka samu daga kungiyar OPEC, a jiya shugaban Rasha Vladimir Putin, da hukumomin makamashi da na tattalin arziki da sauransu sun bayyana cewa, ba su ji mamaki kan wannan labari ba. A wannan rana, yayin da yake ganawa da shugaban kamfanin TOTAL, shugaba Putin ya furta cewa, farashin man fetur zai ragu sakamakon shawarar da kungiyar OPEC ta yanke, wannan ne martani da kasuwanni suka mayar, Rasha ta riga ta yi hasashe kan hakan, kuma tana ganin cewa, babu wata kasar dake fitar da danyen mai data dauki mataki na musamman domin kiyaye farashin man fetur, ciki har da kasar Rasha.(Fatima)