Bisa kididdigar da ma'aikatar gona da albarkatu ta kasar Sin ta fitar, an ce yawan man fetur da gas, da kuma gas da ake samu a kwal ya karu sosai a shekarar 2013, an kuma kara yawan wanda ake hakowa yanzu haka.
A ranar Alhamis din nan, mataimakin darektan ofishin kula da harkokin albarkatu na ma'aikatar gona da albarkatun kasar ta Sin Mista Xu Dachun ya bayyana cewa, bisa aiwatawar da manyan tsare-tsare na daukar matakan inganta ayyukan gano ma'adanai, Sin ta kara karfinta na binciken ma'adinnai, tare kuma da samu babban ci gaba a fannin.
Kididdigar ta ce, a shekarar 2013 yawan sabbin man fetur da Sin ta gano ya kai tan biliyan 1 da miliyan 84, wanda hakan ya sanya shekarar ta 2013, zama shekara ta 11 da aka gano yawan sabbin man fetur fiye da ton biliyan daya, kuma shekara ta 7 a jere, da aka samu sabbin man fetur fiye da ton biliyan guda.(Danladi)