Kasashen Afrika dake kudu da Sahara sun rasa kashi 85 cikin 100 na kasuwancin man fetur tare da Amurka
Harkokin kasuwanci a bangaren man fetur tsakanin kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara da Amurka sun ragu da kashi 85 cikin 100 a shekarar 2015, idan aka kwatanta da na shekarar 2008. Harkar fitar da man fetur na shekara shekara a cikin watan Maris daga kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara da kuma zuwa kasashen dake kudu da hamadar Sahara ta ragu da dalar Amurka biliyan 15 idan aka kwatanta da adadin musanya na dalar Amurka biliyan 100 a shekara da aka samu a shekarar 2008.
A yayin da samar da man fetur a Amurka ke karuwa sosai, nahiyar Afrika ce, ba wai yankin gabas ta tsakiya ba ne ya wahala fiye da sauran kasashen masu fitar da man fetur, in ji wani kwararren Najeriya a man fetur, Victor Eromosele.
Masanin ya danganta wannan ja da baya game da karuwar kasuwancin man fetur tsakanin Afrika da Amurka dalilin ayyukan hakar gas Schiste a kasar Amurka. (Maman Ada)