Kamfanin Total na kasar Faransa ya ba da sanarwa a ranar Alhamis cewa, ya gano rijiyar man fetur da ake sanya fatan alheri kanta a cikin ruwan kwazazzabin San Pedro dake kudu maso yammacin kasar Cote d'Ivoire. Rijiyar binciken man fetur ta Saphir-1XB dake kan yankin CI-514 da kamfanin Total ke aikin kanta ta nuna cewa, akwai dimbin man fetur a yammacin Cote d'Ivoire, in ji wannan sanarwa.
Wannan rijiya da aka gina bisa ayyukan bincike ta tabbatar a karon farko cewa, a cikin kazazzabin San Pedro na yankin hakar man fetur na iyakar Cote d'Ivoire, akwai man fetur. in ji wannan sanarwa dake ambato kalaman darektan ayyukan Total, Marc Blaison. (Maman Ada)