A ranar Talatar nan ne dai Farfesa Jega ya kammala wa'adin aikin na sa a hukumar ta INEC tare da wasu kwamishinonin hukumar su 6.
Yayin wani kwarya-kwaryar taro da ya gudana a helkwatar hukumar ta INEC dake birnin tarayyar kasar Abuja, Jega ya mika ragamar shugabancin hukumar ga babban kwamishinan ta Mohammed Wali dan asalin jihar Sokoto, wanda zai zamo mukaddashin shugaban hukumar gabanin nasa sabon shugaba.
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ne dai ya damka wa farfesa Jega jagorancin hukumar ta INEC a watan Yunin shekarar 2010, bayan cikar wa'adin tsohon shugaban ta Maurice Iwu.
Ya kuma jagoranci manyan zabukan kasar guda biyu, wato na shekarar 2011, da kuma na wannan shekara ta 2015.
Farfesa Jega ya kasance shugaban hukumar zaben Najeriya na farko a tarihi, wanda ya taba gudanar da manyan zabukan kasar har karo biyu.