in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin 'yan ta'adda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama a Nigeriya
2015-07-04 13:13:32 cri
'yan sanda a Nigeriya sun tabbatar a ranar jumma'an nan cewa mutane kusan 10 suka rasu sakamakon harin 'yan kunar bakin wake har sau biyu a Maiduguri babban birnin jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar a ranar alhamis.

Harin kunar bakin waken na farko ya auku ne a kauyen Malari akan hanyar Bama-Kunduga wata mata ce ake zargin ta daure bama baman a jikin ta sannan ta tada shi inda nan take ta hallaka kanta da wadansu mutane guda 7 da tsautsayin ya rutsa da su in ji Kwamishinar 'yan sandar jihar Aderemi Opadokun a hirar ta da manema labarai.

Kwamishinar ta kara da cewa bayan haka mutane 13 sun ji rauni an kuma garzaya da su asibiti.

Sai hari na biyu kuma da ya auku akan titin Alao Dam kusa da hanyar Bama –Kunduga shi ma wata mata ce ake zargin ta nade bam din a jikin ta inda nan take data tayar ta hallaka kanta tare da wadansu mutane 3 dake kusa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China