Jagoran addinin kasar Iran Ayatollah Sayyed Ali Khamenei ya furta a jiya Laraba cewa, kasar Iran ba za ta mika wuya ga matsin lambar da ake mata game da shawarwarin nukiliyarta ba, kana ba za ta amince da bukatun da suka wuce kima da kasashe masu ci gaba suka gabatar mata ba.
Ayatollah Sayyed Ali Khamenei ya bayyana a yayin da yake ba da jawabi a jami'ar Imam Hossein ta kasar Iran a wannan rana cewa, kasashen da suka ci gaba da bukatar samun bayanan kan yadda kasar take bunkasa shirinta na nukiliya, amma kasar Iran din ta ce ba za ta yarda ba. Ya kuma jaddada cewa, kasar Iran ba za ta amince da masu aikin sa ido su duba na'urorinta na soja ba.
Ban da haka kuma, Ayatollah Sayyed Ali Khamenei ya ce, ba za su yarda kasashen waje su sa baki cikin harkokin kimiyar nukiliya da sauran muhimman ayyukan kasar ba.
Ya kuma yi Allah wadai kan yadda kasashen da suka ci gaba da matsa lamba ga kasar,don haka ya nemi gwamnati da hukumar kula da harkokin nukiliya ta kasar Iran da kada su amsa bukatun da suka wuce kima da suka yi musu.(Lami)