in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya nuna matukar takaicinsa bisa rashin cimma nasarar hana yaduwar makaman nukiliya
2015-05-24 17:10:14 cri
Babbar magatakardar MDD Ban Ki-moon ya bayyana matukar takaicin sa, bisa rashin cimma nasarar da ake fata, ta rage yaduwar makaman Nukiliya a duniya.

Mr. Ban ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da aka fitar game da taron nazarin yarjejeniyar hana yaduwar makaman na nukiliya karo na 9 a jiya Asabar.

Sanarwar ta ce masu ruwa da tsaki game da yarjejeniyar, ba su rattaba hannu kan batun kafa yankin Gabas ta Tsakiya maras makaman nukiliya, da sauran manyan makamai ba. Game da wannan batu, mista Ban ya bayyana matukar damuwarsa, sai dai duk da hakan ya ce zai ci gaba da sa kaimi ga gudanar shawarwari cikin juriya da hakuri tsakanin shiyya-shiyya, a kokarin cimma wannan buri cikin gaggawa.

A sa'i daya kuma, mista Ban ya yi kira ga kasashen da wannan batu ya shafa, da su ci gaba da kasancewa yadda suke a shekaru 5 da suka gabata, su kuma kara kokari a fannonin rage yawan makaman nukiliya, da yaki da yaduwar wadannan makamai da dai sauran muhimman batutuwa.

A ranar 22 ga watan ne aka rufe taron nazarin yarjejeniyar hana yaduwar makaman na nukiliya karo na 9 a birnin New York, hedkwatar MDD. Kuma ba a kai ga cimma sakamako a yayin taro ba, saboda tarin bambance-bambance tsakanin wasu kasashe a fannin kafa yankin Gabas ta Tsakiya maras makaman nukiliya, da kuma sauran manyan makamai. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China