Sassa daban daban mahalarta taron sun yaba wa yarjejeniyar a kan yadda ta taimaka a kiyaye zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali a duniya, sa'an nan sun bayyana goyon bayansu game da kwance damarar nukiliya da hana yaduwar makaman nukiliya da kuma yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana da aka tsara cikin yarjejeniyar, tare da inganta kwarjinin yarjejeniyar da kuma ingancinsa.
Sai dai sakamakon yadda wasu kasashe ke fama da babban sabanin ra'ayi a kan kafa yankin rashin kasancewar makaman nukiliya da sauran manyan makaman kare dangi a yankin gabas ta tsakiya, taron ya kasa cimma wata yarjejeniya a kan batun.
Tawagar wakilan kasar Sin ta halarci taron a karkashin jagorancin mataimakin ministan harkokin waje na kasar Mr.Li Baodong, wanda ya gabatar da jawabi a yayin babbar mahawarar taron. A yayin taron, tagawar kasar Sin ta bayyana matsayin kasar a kan wasu muhimman batutuwa.
A kan kira taron nazarin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya a shekaru biyar biyar, kuma an fara taron na wannan karo a ranar 27 ga watan Afrilun da ya gabata.(Lubabatu)