in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta jaddada matsayin NPT ga kasar da ke son zama mamban NSG
2015-06-04 09:43:46 cri

Kasar Sin ta sake jaddada cewa, kungiyar masu samar da makaman nukiliya (NSG) tana jaddada muhimmancin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukuliya (NPT) a matsayin ka'idar karbar kasa cikin mambar kungiyar.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying ce ta bayyana hakan yayin da take amsa tambayar wakilin kamfanin dillancin labaran Associated Press na Pakistan game da matsayin kasar Sin kan takardar da Pakistan ta gabatar ta neman zama mamba a kungiyar ta NSG yayin zaman taronta da ya gudana a kasar Argentina.

Madam Hua ta ce, kungiyar ta NSG kungiya ce mai muhimmanci da ta dade tana kokarin hana yaduwar makaman nukiliya a duniya. Ta ce, kasar Sin ta yi imanin cewa, wannan batu na Pakistan yana bukatar dogon nazari tsakanin mambobin kungiyar, ta yadda za a cimma matsaya daga karshe.

Ta ce, kungiyar na maraba da shigar kasar Pakistan cikin wannan kungiya, kuma tana fatan hakan zai kara taimakawa kokarin kungiyar na hana yaduwar muggan makamai a doron kasa.

Baya ga kasar Pakistan ma akwai wasu kasashen da ba su sanya hannu cikin wannan yarjejeniya ba da suka nuna sha'awarsu ta shiga wannan kungiya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China