in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta halarci shawarwari game da yarjejeniyar nukiliyar Iran
2015-05-14 20:18:16 cri

Cheng Jingye, jakadan kasar Sin a kungiyar wakilan kasar a birnin Vienna zai halarci sabon shawarwari tsakanin manyan jami'an harkokin siyasa kan daddale cikakkiyar yarjejeniya dangane da batun nukiliyar Iran, kamar yadda Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a yau Alhamis a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing.

Ta kara da cewa, ban da kasar Sin, kasashen Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Jamus, kungiyar tarayyar Turai da Iran su ma za su gudanar da shawarwarin a Vienna.

Madam Hua ta ci gaba da cewa, yanzu ana duba tanade-tanaden da ke cikin cikakkiyar yarjejeniyar. Kasar Sin na fatan sassa daban daban masu ruwa da tsaki za su yi amfani da wannan dama, wajen kai zuciya nesa ta fuskar siyasa, su nuna wa juna girmamawa da kulawa, a kokarin warware batun yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China