An bude taron wakilan kungiyar yara ta kasar Sin karo na 7 a nan birnin Beijing, inda shugaban kasar Sin Mr Xi Jinping ya gana da dukkan wakilai tare da yi masu kyakkyawan fata na koyon ilmi yadda ya kamata a lokacinsu, kuma ya nanata cewa, lokacin yara na da muhimmanci sosai ga rayuwar kowa don haka ya kamata kananan yara sun tsai da burin su mai kyau da koyon dabi'a da tunani da biyayya mai kyau ta yadda za su bautawa kasar nan gaba, hakazalika, shugaba Xi ya yi kyakkyawan fata ga kananan yara don ganin za su yi rayuwa mai kyau nan gaba da cimma mafarkin kasar Sin. (Amina)