in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Indiya a birnin Xi'an
2015-05-14 16:40:43 cri
Da yammacin yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Indiya Narendra Modi wanda ke ziyarar aiki a nan kasar Sin a birnin Xi'an.

A yau da safe ne Mr. Narendra Modi ya isa birnin Xi'an don fara ziyarar aiki ta kwanaki uku a nan kasar Sin. Da isarsa birnin Xi'an, Mr. Modi ya ziyarci wurin adana mutum-mutumin mayakan nan na Tarakota wato soja da dawakai na zamanin daular Qin da gidan addinin Buddha na Daxing.

Ban da birnin Xi'an, Mr. Modi zai kuma iso nan birnin Beijing, da birnin Shanghai, wato cibiyar hada-hadar kudi ta kasar Sin. A lokacin da yake ziyara a wadannan birane, zai kuma yin ganawa da al'ummomi daban daban na kasar Sin.

Wannan ne karo na farko da Mr. Modi ya kawo ziyara kasar Sin tun bayan da ya zama firaministan kasar Indiya. Ana sa ran cewa, wannan ziyarar da Mr. Modi ke yi a kasar Sin za ta kara karfafa sabuwar dangantaka a tsakanin kasashen biyu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China