Bayan isowarsa kasar a Lahadin nan, shugaba Xi ya bayyana fatan cewa ziyarar tasa, za ta kyautata dangantakar dake tsakanin Sin da Belarus, ta yadda hakan zai dada taimakawa jama'ar kasashen biyu.
Xi Jinping ya isa kasar Belarus ne, bayan kammala ziyara a kasar Rasha, inda ya halarci bikin tunawa da cika shekaru 70 da cimma nasarar kare kasar ta Rasha. (Maryam)