Wang Yi ya ce, akwai muhimman batutuwa guda 2 a cikin ziyarar da shugaban kasar Sin Xi ya yi a kasashen Turai da Asiya na wannan karo, batu na farko shi ne, a yi kokari tare da jama'a masu kaunar zaman lafiya da kishin kasa don tunawa da cika shekaru 70 da samun nasarar yaki da masu tsattsauran ra'ayi na Fascism a duniya. Batu na biyu shi ne, a ci gaba da kafa amincewar juna a fannin siyasa da karfafa hakikanin hadin gwiwa da kasashen Rasha, Kazakhstan, da Belarus, don gaggauta hadin kai tsakanin ra'ayin yankunan tattalin arziki dake hanyar Siliki, da dabarun raya kasashe 3 bai daya.
Wang Yi ya ce, yayin da kasashen duniya ke karkata hankalinsu game da zaman lafiya da samun bunkasuwa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga kasashen duniya da su nazari tarihi da kiyaye zaman lafiya da kokarta raya kasashensu, kuma Sin za ta yi hadin gwiwa da jama'ar kasashen duniya, don kafa sabon nau'in dangantakar kasa da kasa ta hadin gwiwa da samun moriyar juna, kuma wannan ba ma kawai ya samu amincewar wadannan kasashe 3 ba, har ma ya samu jinjinawa daga kasashen duniya.(Bako)