Mataimakin shugaban sashen nazarin yankin gabashin Rasha da kasashen dake dab da yankin na kwalejin nazarin kasar Rasha Andrei Ostrovsky ya ce, ana sa ran sosai game da hadin gwiwa a fannoni daban daban dake tsakanin kasashen Rasha da Sin, kuma hadin gwiwar bangarorin biyu za ta inganta ci gaban shiyya-shiyya da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai SCO da kuma kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki na kasashen Turai da Asiya wato EEU.
Shugaban asusun kula da kudancin tekun Asean na kasar Indonesiya Bambang Suryono, ya ce, ziyarar shugaban Xi a bikin cika shekaru 70 da samun nasarar yakin kare kasar Rasha za ta kara sanin jama'ar kasashen duniya game da gudummawar da Sin ta bayar game da babbar hasarar da ta samu a lokacin yakin duniya na biyu, kuma abun ya nuna matsayi guda da Sin da Rasha ke tsayawa wajen kare sakamakon da aka samu wajen yaki da masu tsattsaran ra'ayi na Fascism, kuma yana da ma'anar musamman wajen ci gaba da shimfida adalci a duniya, da yaki da ra'ayin nuna karfin tuwo a duniya.
Direktan kwamitin kula da batutuwan duniya na Rasha Kortunov ya ce, Sin kasa ce da ita ma ta yi hasarar mutane sosai cikin yakin duniya na 2. A kasashen yammacin duniya, mutane sun san tarihin yakin duniya na biyu a fagen daga dake kasashen Turai, amma ba su da masaniya game da fagen daga dake yankunan Asiya da tekun Fasific. Ziyarar shugaban Xi a wannan karo, zai kara sanin jama'a game da gudummawar da Sin da tsohuwar Soviet Union suka yi, kuma zai amfanawa matasa da su san tarihi daga duk fannoni.(Bako)