A yayin ganawar da shugabannin biyu suka gudanar a jiya Asabar, Xi Jinping ya bayyana cewa a bara, an gudanar da bikin cika shekaru 70 da cimma nasarar yaki da hare-haren sojojin Japan a kasar Sin, yayin da kuma aka gudanar da bikin tunawa da cika shekaru 70, da cimma nasarar yakin duniya na biyu a kasar Rasha, bukukuwan da za su ci gaba da kasancewa darasi ga kasashen duniya tsahon tarihi.
A cewar da wadannan bukukuwa za kuma su kasance wata dama, ta tunawa da wadanda suka rasa rayukansu sakamakon yake-yake, tare da ginshikin ayyukan da ake gudanarwa a fannin kiyaye zaman lafiya, da kuma kare makomar kasashen biyu.
Bugu da kari shugaba Xi ya jaddada cewa, bunkasuwar dangantakar abota tsakanin Sin da kasar Rasha, na samun goyon baya mai karfi daga manufofinsu na siyasa, da kuma amincewar jama'ar kasashen biyu, kana hakan ya dace da bukatun kasashen. Daga nan sai ya yi fatan ganin kasashen biyu sun ci gaba da habaka hadin gwiwar dake tskaninsu yadda ya kamata, domin samun karin sakamako mai kyau, da kuma samar da karin tallafi ga al'ummominsu.
A nasa bangaren kuwa, Mr Medvedev ya ce kasar Rasha na da burin zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin, musamman a fannonin zuba jari, da sha'anin kudi, da makamashi. Baya ga batun tabbatar da kafuwar shirin zirin tattalin arziki na siliki, tare da ci gaban kawancen tattalin arziki na Turai da Asiya. Har wa yau Rashan na fatan karfafa mu'amalar kasashen biyu, a fannonin al'adu da kuma harkokin soja. (Maryam)