Shugaban Xi ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manyan jami'ai daga larduna 7 na gabashin kasar wadanda suka hada da Shanghai, Anhui, Fujian, Jiangsu, Jiangxi, Shandong da kuma Zhejiang.
Don haka ya ce, kamata ya yi gwamnatoci a dukkan matakai su kalli muhimman abubuwa da tsarin tattalin arziki da kuma batun ci gaban jin dadin jama'a yadda ya kamata.
Xi wanda har ila yau shi ne babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS ya je Zhejiang ne a rangandin aikin da yake, inda kuma ya taba zama shugaban jam'iyyar a wurin daga shekarar 2002 zuwa 2007.
Wannan dai ita ce shekarar karshe a cikim shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 12 kuma gwamnatin tsakiya na duba yiwuwar tsara shiri na 13. (Ibrahim Yaya)