A Litinin din nan ne dai aka kaddamar da taron shekara-shekara karo na farko, na wannan dandali na hadin gwiwa mai zaman kan sa. Cikin jawabin na sa Mr. Xi ya bayyana imanin sa ga wannan taro.
Xi Jinping ya kuma yi nuni da cewa, bayan kafa kafuwar dandalin hadin gwiwa da amincewa juna na Asiya CICA yau shekaru 23 da suka gabata, an yi kokari wajen samun ci gaba, a fannin aiwatar da matakan nuna imani da juna, da sa kaimi ga yin shawarwari a tsakanin kasashen yankin, da kuma samun bunkasuwa tare da dai sauransu. Ya ce dandalin ya riga ya kasance muhimmin tsari na neman tabbatar da tsaron nahiyar Asiya.
An mayar daTaken taron a wannan karo shi ne "nahiyar Asiya a shekaru 10 masu zuwa: kiyaye tsaro da samun bunkasuwa a nahiyar Asiya a shekaru 10 masu zuwa" a matsayin babban taken taron, wanda ke da burin sake tunanin. Kaza lika burin taron shi ne sa kaimi ga la'akari da batun tabbatar da zaman lafiya, da samun bunkasuwa a Asiya a sabon yanayi.
Xi Jinping ya yi fatan bangarori daban daban za su tattauna da juna, tare da mu'amala tare, a kokarin bayar da shawarwari ga wajen samar da gudummawar aikin sa kaimi ga tabbatar da makomar bai daya, da zaman lafiya, da kuma samun bunkasuwa a nahiyar Asiya. (Zainab)