A lokacin da ya kai ziyara kasar indiya a watan Satumban bara ne, shugabannin biyu suka cimma muhimman yarjejeniyoyi wajen bunkasa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare da batun gina layin dogo da yankin masana'antu, karfafa musaya da kula da kan iyakokinsu da sauran batutuwan da suka shafi kasa da kasa da shiyya-shiyya.
A jawabinsa Mr. Modi ya yi imanin cewa, wannan ziyara za ta bunkasa hadin gwiwar bangarorin biyu wadda za ta kai ga cimma sabon ci gaba.
A gobe ne ake sa ran Mr Modi zai gana da takwaransa na kasar Sin Li Keqiang da shugaban majalisar wakilan jama'a Zhang Dejiang a nan birnin Beijing. (Ibrahim Yaya)