in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Belarus
2015-05-11 09:48:21 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari taregana da shugaban takwaransa na kasar Belarus Alexandr Lukashenko a jiya Lahadi 10 ga wata a birnin Minsk, fadar mulkin kasar Belarus, inda suka amince da kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban, da aiwatar da manufofin raya kasashen biyu da kuma bude sabon lokacinkokarin shiga wani sabon zamani na raya dangantakar abokantaka huldar abokai a tsakanin su bisa manyan tsare-tsare.

Kana shugabannin biyu sun gana da 'yan jarida jaridu tare, inda Xi Jinping ya yi nuni da cewa, sun amince da yin amfani da damar gina zirin tattalin arziki na siliki tare wajen zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu. Kuma sun tsaida kudurin kara yin mu'amalar al'adu a tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangare, Shugaba Lukashenko ya bayyana cewa, ziyarar shugaba Xi Jinping a kasar Belarus wannan karo tana da babbar ma'ana. Kasashen biyu sun daddale yarjejeniyar hadin gwiwar sada zumunta a tsakaninsu, inda aka tsaida kudurin kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin tattalin arziki, sufuri, zuba jari da dai sauransu. Haka kuma yace zasu kara yin mu'amala da hadin gwiwa kan harkokin kasa da kasa da yankuna. Kasar Belarus ta na goyon baya da n shiga shirin zirin tattalin arziki na siliki da kasar Sin take kirayi don a gudanar da shi yi kira. Har ila yau Shugaban na Kasar Belarus ya lura da cewa, kasashen biyu sun sadaukar da kai da bada gudummawa wajen cimma nasarar yakin duniya karo na biyu, don haka kasashen biyu za su tuna da cika shekaru 70 da ture ra'ayin FascismFansics a shekarar bana tare. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China