A lokacin ganawar tasu, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, an raya dangantakar dake tsakanin Sin da Belarus cikin sauri, kana an fadada hadin gwiwarsu sosai. Yana mai lura da cewa, a shekarun baya baya nan, yawan cinikin dake tsakanin Sin da Belarus ya kara karuwa. Kana ana fuskantar kyakkyawar makoma kan hadin gwiwarsu a fannin tattalin arziki da cinikayya. A don haka in ji shi, kasar Sin tana son ci gaba da yin kokari tare da kasar Belarus wajen fadada ciniki, kyautata tsarin yin ciniki, da kuma sa kaimi ga samun daidaito a yayin ciniki.
A nasa bangare, Kobyakov ya bayyana cewa, kasar Belarus abokiyar kasar Sin ce, kuma tana goyon bayan shirin zirin tattalin arziki na siliki da kasar Sin ta gabatar, da gaggauta musayar mutane da jari a yankin, tare kuma da sa kaimi ga samun bunkasuwar babban yankin Asiya da Turai.
Hakazalika kuma, duk a wannan rana ta Litinin 11 ga wata a birnin na Minsk, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban majalisar dattijan kasar ta Belarus, Mikhail Myasnikovich da kuma shugaban majalisar wakilan kasar Vladimir Andreichenko. (Zainab)