Kwamitin gudanarwa na kungiyar tarayyar Turai EU, ya ce kungiyar za ta kara samarwa kasar Afirka ta tsakiya kudaden tallafi har Euro miliyan 72.
Kungiyar ta bayyana hakan ne yayin taron kasa da kasa game da harkokin nahiyar Afrika ta tsakiya, taron da ya gudana a ranar 26 ga watan nan a birnin Brussel.
Rahotanni sun nuna cewa wannan shirin da ake gudanarwa na kunshe da tallafin jin kai, wanda karkashin sa za a kara samarwa kasar kimanin Euro miliyan 10. Kaza lika EU na da burin kara kasafin kudinta na taimakawa, ya zuwa Euro miliyan 40. A sa'i daya kuma, za a kara zubawa kasar Euro miliyan 22 a fannin asusun zuba jari. Hakan kuma, akwai yiyuwar EUn ta ci gaba da kara ba da tallafi ga Afirka ta tsakiya a nan gaba.
Taron da aka yi a wannan karo na da zummar sanya kasashen duniya kara mai da hankali kan halin da Afrika ta tsakiya ke ciki, tare da kara baiwa mata taimako yadda ya kamata.
Taron na wannan karo dai ya samu halartar mukadashin shugabar kasar Afrika ta tsakiya Madam Catherine Samba-Panza, da wakilai daga kasashen Faransa, da Jamus, da Holland da dai sauran kasashe. (Amina)