Wannan dandali dai zai kunshi duk wasu bayanai, da suka shafi harkokin raya zirga-zirgar jiragen sama a nahiyar Afirka, kana kamfanoni daban daban na Sin, za su yi amfani da fiffikon su wajen inganta hadin gwiwa a fannin zirga-zirgar jiragen sama, tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.
Bisa labarin da aka bayar, an ce a shekarar 2014, Sin ta gabatar da shirin raya hadin gwiwa zirga-zirgar jiragen sama tsakanin ta da kasashen Afrika. Yanzu kuma Sin na gudanar da hadin gwiwa da kasashen na Afrika, a fannin fitar da jiragen sama na sufurin jama'a, da hadin gwiwa tsakanin kamfanonin jiragen sama, da raya muhimman ababen more rayuwa a filayen jiragen sama, da kuma horas da ma'aikata da sauransu. Duka dai da nufin ci gaba da aiwatar da wannan shiri, na hukumar CAAC, tare da hadin gwiwar sauran sassan da abun ya shafa. (Bako)