in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sarkin Zulu ya yi kira da a kawo karshen kyamar baki a Afrika ta Kudu
2015-04-21 11:06:15 cri
Basaraken gargajiya na al'ummar Zulu dake kasar Afirka ta Kudu Goodwill Zwelithini, ya bayyana bukatar kawo karshen tashin hankalin kyamar baki da aka shafe kwanaki da dama ana aiwatarwa a kasar.

Sarkin a Zulu ya bayyana hakan ne cikin jawabin da ya gabatar a jiya Litinin, yayin taron gangamin 'yan kabilar ta Zulu da aka gudanar a birnin Durban.

Zwelithini ya ce, yanzu abun da ya fi muhimmanci shi ne farfado da zaman lafiya, yana mai cewa, aika-aikar da wasu gungun 'yan kasar suka aikata ta keta hakkin dan Adam, inda ya bukaci a gurfanar da wadanda ke da hannu cikin wannan ta'asa gaban kuliya.

Bugu da kari, sarkin ya bukaci al'ummar kasar da su tattauna game da hanyoyin da za su bi wajen wanzar da zaman jituwa da baki, yana mai kira ga gwamnatin kasar da ta tsara dokoki, wadanda za su tabbatar da kyakkyawar zamantakewa tsakanin baki da sauran al'ummar kasar.

Zwelithini ya sake musunta zargin da aka yi masa na rura wutar kyamar baki a kasar, inda ya ce, akwai wasu mutane dake kulla wata makarkashiya ta daban, don haka ya zama dole Afirka ta Kudu ta yi hattara.

A karshe ya bukaci kwamitin kare hakkin dan Adam na kasar da ya yi bincike game da wannan lamari na kyamar baki, tare da kaucewa murde gaskiya, yayin da ake hada rahotanni game da furucinsa. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China