A wannan rana, kwamitin sulhu na M.D.D. ya yi taro game da halin da ake ciki a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, inda aka zartas da wani kuduri cewa, bisa bukatar sakatare-janar na M.D.D. Ban Ki-moon, ban da kiyaye yawan 'yan kungiyar da aka tanada cikin kuduri mai lamba 2149, za a kara tura wasu zuwa wannan kasa.
An ce, Ban Ki-moon ya mika wa shugaban kwamitin sulhu na M.D.D.wata wasika a ranar 29 ga watan Janairu na bana, inda ya bayyana cewa, ganin yanayin rashin tabbas da ake ciki a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, da rikicin da ke ci gaba a tsakanin dakarun fararen hula masu aikin sa kai ta fuskar aikin tsaro Anti-Balaka da tsohon 'yan kungiyar Seleka, ana bukatar karin sojoji don tabbatar da tsaro.(Bako)