in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Afrika ta Kudu ya gana da ministan harkokin wajen Sin
2015-04-16 10:39:40 cri

A jiya Laraba 15 ga wata, a fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu da ke birnin Cape Town, shugaban kasar Jacob Zuma ya gana da ministan harkokin wajen Sin Wang Yi da ya kai ziyara a kasar.

Da farko, ministan Wang ya mika gaisuwa da fatan alheri da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika wa takwaransa na Afrika ta Kudu, sannan ya bayyana cewa, kasashen Sin da Afrika ta Kudu abokai ne bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, kuma sun samu hadin gwiwa masu gamsarwa. Ya kara da cewa a nan gaba, bangarorin biyu za su ci gaba da daukar matakai da suka dace don tabbatar da ra'ayin bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, don canza amincewar juna a tsakaninsu daga fannin siyasa zuwa sabon kuzarin da zai karfafa hadin gwiwar moriyar juna tsakaninsu.

Wang Yi ya kuma kara da cewa, a yayin taron tattaunawar hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika wato FOCAC karo na shida da za a yi a Afrika ta Kudu na bana, kasar Sin za ta ci gaba da hadin gwiwa da Afrika ta Kudu, don kokarta harhada sana'o'in kasashen biyu da inganta hadin gwiwa a fannin makamashi tsakaninsu, da kafa tsarin kiwon lafiya a Afrika, da sa kaimi ga samar da zaman lafiya da lumana a nahiyar Afirka, ta hakan za a mayar da taron FOCAC a matsayin wani gaggarumin dandalin hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.

A nasa bangare kuma, Jacob Zuma ya mika gaisuwa ga takwaransa na kasar Sin Xi Jinping ta ministan Wang, kuma ya amince da shawarar da kasar Sin ta gabatar wajen inganta hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu, ya kuma jinjina taimakon da kullum Sin ke baiwa Afrika ta Kudu wajen samun ci gaba. Shugaban Zuma ya kara da cewa, Afrika ta Kudu tana fatan ci gaba da inganta hadin gwiwa da Sin, musamman ma wajen harhada sana'o'in kasashen biyu, da karfafa hadin gwiwa a fannin makamashi a tsakaninsu, Afrika ta Kudu ma na sa ran inganta hadin gwiwa da Sin, don tabbatar da shirya taron FOCAC cikin nasara a bana.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China