in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan karuwar tattalin arziki na yankin dake kudu da hamadar Sahara zai rage zuwa kashi 4 cikin 100 a bana, in ji bankin duniya
2015-04-14 10:33:18 cri
Bisa wani rahoton da bankin duniya ya fitar, a jiya Litinin 13 ga wata, an ce, sabo da raguwar farashin man fetur da na sauran manyan kayayyaki a kasuwannin kasa da kasa, an yi kiyasta cewa, yawan karuwar tattalin arziki na yankin kudu da hamadar Sahara zai kai kashi 4 cikin 100 a bana. Idan aka kwatanta jimillar da kashi 4.5 cikin 100 ta bara, ke nan jimillar ta ragu.

A jiya Litinin, bankin duniya ya gabatar da wani rahotonsa na rabin shekara a birnin Nairobi hedkwatar kasar Kenya cewa, bisa hasashen da aka yi, yawan karuwar tattalin arziki na yankin kudu da hamadar Sahara zai yi kasa da matsaikacin yawan karuwar tattalin arziki na yankin cikin shekaru 20 da suka gabata.

Rahoton ya ce, faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya zai kawo babbar illa ga kasashe kamarsu Angola da Equatorial Guinea wadanda ke dogara ga fitar da mai sosai, don haka wadannan kasashe za su aiwatar da manufar tsuke bakin aljihu. A nasu bangare ma, kasashen Cote D'ivoire, Kenya, da Senegal wato kasashen dake shigar da man fetur, tattalin arzikinsu zai ci gaba da habaka, yayin da matsalar hauhawar farashin kayayyaki da yadda ake daidaita manufofin kudi zai ci gaba da yin daibaibayi a kasar Ghana, kuma matsalar wutar lantarki za ta zama abun da zai hana ruwa gudu game da raya tattalin arziki na Afrika ta Kudu.

Mataimakin shugaban bankin duniya dake yankin Afrika Abdoulaye Makhtar Diop, yace duk da cewa batun raya yankin kudu da hamadar Sahara ya gamu da sabbin kalubaloli da dama, amma tattalin arziki na yankin zai ci gaba da samun karuwa.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China