in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
"Sin da Afrika za su karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu", in ji jakadan Kuang
2015-03-20 11:06:08 cri
Jakadan Sin a kungiyar AU Kuang Weilin, ya ce, kasar Sin tana sa ran karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kungiyar AU da ma sauran kasashen Afrika ta hanyar kafa ofishin jakadancin din-din-din a kungiyar.

Jakadan Kuang, wanda ya dade yana harkokin diplomasiyya, ya bayyana ma manema labaru cewa, dalilin da ya sa aka kafa ofishin jakadancin Sin a AU shi ne, domin cika alkawuran da shugaban kasar Sin Xi Jinping da firaministan kasar Li Keqiang suka dauka, yayin da suka ziyarci nahiyar Afrika. Mista Kuang ya ce, zai yi kokarin lalubo sabuwar hanyar inganta hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu a fannonin kawar da talauci, da samar da guraben ayyuka yi ga jama'ar Afrika.

A nata bangare, Madam Nkosazana Dlamini-Zuma, shugabar kwamitin kungiyar AU ta bayyana cewa, matakan da Sin ta dauka ya kafa tarihi, kuma bangarorin biyu za su kara samun babbar dama wajen inganta hadin gwiwar don moriyar juna tsakaninsu.

Jakada Kuang ya kara da cewa, a lokacin da firaministan Sin Li Keqiang ya ziyarci Afrika a bara, ya ce, Sin za ta kara hadin gwiwa da kasashen Afrika game da muhimman ababen more rayuwa da sauran manyan fannoni. Domin cika alkawarin da firaministan Sin ya dauka, ofishin jadakancin Sin a AU zai ci gaba da hadin gwiwa da kasashen Afrika a fannin siyasa, tattalin arziki, al'adu, da tsaro da sauransu, don karfafa hadin gwiwa tsakaninsu daga duk fannoni.Ya gaya wa manema labaru cewa, yanzu, ofishin jakadancinsa na shawarwari da AU, don tura wata tawagar AU zuwa kasar Sin da muradun ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China