Kwamitin sulhu na MDD ya zartas da wani kuduri a Talata 28 ga wata, inda ya yanke shawarar kara wa'adin aikin tawagar musamman na majalisar dake Afrika ta tsakiya MINUSCA da tsawon shekara daya wato zuwa ga karshen watan Afrilu na shekarar badi.
Kudurin ya kuma bayyana cewa, majalisar na ganin cewa, halin da kasar ke ciki zai ci gaba da kawo illa ga zaman lafiya da tsaro ga wannan yanki, hakan ya sa aka yanke wannan shawara.
An ba da labarin cewa, Afrika ta tsakiya na fama da rikici cikin dogon lokaci, 'yan kungiya masu tsattsauran ra'ayi ta anti-Balaka da mambobin tsohon kungiyar Seleka suna tada rigingimu tsakaninsu, lamarin da ya haifar da kalubalen jin kai mai tsanani a kasar.
Hakan ya sa, kudurin ya nemi bangarorin daban-daban masu ruwa da tsaki da su magance sanya shinge ga aikin tawagar MINUSCA tare da bin ka'idar ba da tallafin jin kai da majalisar ta tsara, gami da dokokin kasa da kasa, ta yadda za a samar da tallafin jin kai cikin lokaci ga wadanda ke da bukata, musamman ma wasu 'yan gudun hijira. (Amina)